Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, a daidai lokacin da tattaunawar diflomasiyya ke fuskantar rashin tabbas a yankin na Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, amma har yanzu ba a kai ga cimma wata matsaya ba.
Ana kuma fargabar cewa wannan zargi zai ƙara dagula zaman tattaunawar da ake shirin yi a Pakistan, inda ake sa ran bangarorin biyu za su gana.
Trump ya kuma nuna rashin gamsuwa da tsawon lokacin tattaunawar, yana mai gargadin cewa idan ba a cimma yarjejeniya ba cikin lokaci, za a iya komawa ga matakin soja.
Sai dai a gefe guda, Iran na zargin Amurka da ita ce ke karya yarjejeniyar, musamman kan batun toshe hanyoyin ruwa da kuma matakan soji da take ɗauka.
Masana na ganin cewa wannan musayar zargi tsakanin ɓangarorin biyu na nuna yadda yarjejeniyar tsagaita wutar ke cikin rauni, tare da yiwuwar rikicin ya sake ɓarkewa idan tattaunawar ta gaza.
