DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya kori ministocinsa biyu

Shugaba Tinubu ya kori ministocinsa biyu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauke Ministan Kudi kuma mai kula da tattalin arziki, Wale Edun, tare da Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmad Musa Dangiwa.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce an umarci Edun da ya mika ragamar aiki ga Taiwo Oyedele, wanda yanzu zai karɓi mukamin Ministan Kudi kuma mai kula da tattalin arziki.

Kafin wannan naɗi, Oyedele ya kasance karamin Minista a Ma’aikatar Kudi.

Haka kuma, an bayyana Muttaqa Rabe Darma a matsayin wanda aka zaɓa domin zama Ministan Gidaje da Raya Birane, yayin da aka umarci Dangiwa da ya mika aiki ga karamin Ministan a ma’aikatar.

Sanarwar ta ce dole ne a kammala dukkanin miƙa da karɓar aiki kafin ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.

Akume ya ce sauye-sauyen na da nufin ƙarfafa haɗin kai da inganta aiki a gwamnati domin samar da sakamako mai tasiri ga tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa shugaban Nijeriya ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen aiwatar da wannan sauyi.

Shugaba Tinubu ya gode wa ministocin da aka sauke bisa hidimarsu, tare da yi musu fatan alheri a gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata