Gwamnatin Jihar Kebbi ta caccaki tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, kan matakinsa na shiga takarar gwamna a 2027, tana mai zarginsa da ƙin faɗin gaskiya game da halin da jihar ke ciki.
A wata sanarwa da mai bai wa gwamna Nasir Idris shawara kan yada labarai, Yahaya Sarki, ya fitar ranar Lahadi, gwamnatin ta ce Malami na da ’yancin tsayawa takara, amma ba za ta yi shiru kan “kalaman karya” da ya yi wajen bayyana dalilin shiga takarar ba.
Gwamnatin ta ce Malami ya ambaci matsalolin tsaro, talauci, rashin ingancin ilimi da matsin tattalin arziki a matsayin dalilan shiga takarar, amma ya manta cewa yana cikin wadanda suka jagoranci kasar har zuwa shekaru uku da suka gabata kuma suke da hannu a matsalolin da ake fama da su yanzu.
Sanarwar ta zargi tsohon ministan da fifita kansa a lokacin da yake kan mulki maimakon kokarin magance matsalolin jama’a, tana mai cewa matsalolin tsaro da talauci sun kara tsananta ne sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci a baya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin ta kuma yi zargin cewa wasu daga cikin tsofaffin shugabanni sun koma attajirai cikin kankanin lokaci yayin da kasar ke fuskantar matsaloli da tabarbarewar tattalin arziki.
Dangane da kalaman Malami kan ilimi da tsaro, gwamnatin ta ce matsalolin sun kai munanan matakai ne kafin gwamnatin Nasir Idris ta hau mulki a 2023, tana mai cewa yanzu ana aiwatar da gyare-gyare a bangarorin ilimi, lafiya, noma, hanyoyi da tsaro.
Ta bayyana cewa an gina sabbin azuzuwa, an dauki malamai 2,000 aiki, yayin da ake gyaran asibitoci 31 da cibiyoyin lafiya 21 a fadin jihar, tare da samar da kayan aikin zamani a wasu cibiyoyin lafiya.
A bangaren tsaro kuwa, gwamnatin ta zargi Malami da yin shiru yayin da ta’addanci da fashi suka karu a lokacin da yake rike da mukamin Antoni Janar, tana mai cewa wadanda suka haddasa matsalolin baya bai kamata su nemi sabon mukami ba.
