DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeKetarePutin na Russia ya ce yaki da Ukraine na dab da zuwa...

Putin na Russia ya ce yaki da Ukraine na dab da zuwa karshe

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa yakin Ukraine na dab da karewa, yana mai zargin kasashen Yamma da kara ruruta rikicin ta hanyar bai wa Ukraine tallafin soja.

Putin ya bayyana hakan ne ranar Asabar bayan bikin tunawa da nasarar Tarayyar Soviet a Yakin Duniya na Biyu, inda ya ce sojojin Rasha na fafatawa da “karfi mai hatsari” da kasashen NATO ke marawa baya a Ukraine.

Kalaman nasa sun zo ne yayin da aka fara tsagaita wuta na kwanaki uku da Amurka ta shiga tsakani wajen samarwa, duk da cewa Rasha da Ukraine sun rika zargin juna da karya yarjejeniyar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana fatan tsagaita wutar zai zama “farkon kawo karshen” yakin da aka shafe shekaru ana yi, yana mai cewa bangarorin biyu sun amince da musayar fursunoni 1,000 kowanne.

Sai dai Putin ya ce har yanzu Rasha ba ta samu wata shawara daga Ukraine ba kan yadda za a gudanar da musayar fursunonin, yana mai cewa ba a shirya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar ba a yanzu.

A jawabin da ya yi a Moscow, Putin ya sake jaddada cewa manufofin Rasha a yakin Ukraine “adalci ne”, yana mai cewa kasashen Yamma sun yi tsammanin Rasha za ta durkushe amma hakan bai faru ba.

Bikin na bana ya kasance cikin tsauraran matakan tsaro sakamakon hare-haren Ukraine a baya-bayan nan, inda aka rage girman fareti kuma ba a nuna manyan makaman soja kamar yadda aka saba ba.

Yakin Rasha da Ukraine wanda ya shiga shekara ta biyar ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, yayin da tattaunawar sulhu da Amurka ke jagoranta har yanzu ba ta samu gagarumar nasara ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata