Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Muhammad Dan’iya, ya zama dan takarar gwamna a sabuwar tafiyar jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027 a jihar.
Dan’iya, wanda na kusa ne ga tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal kuma tsohon mataimakin sa, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da tsohon sakataren yada labaransa, Aminu Abubakar, ya fitar da safiyar Juma’a.
Tsohon mataimakin gwamnan ya gode wa shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da magoya baya bisa amincewar da suka nuna masa wajen ba shi damar jagorantar tafiyar ADC a jihar.
Dan’iya, wanda ke rike da sarautar Walin Sokoto, ya bayyana fitowar sa a matsayin babban nauyi tare da alkawarin yin aiki domin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban jihar Sokoto.
Ya kuma yaba wa Aminu Waziri Tambuwal bisa goyon baya da shawarwarin da ya rika ba shi, yana mai cewa gudunmawar da dattawa, matasa, mata da sauran magoya baya suka bayar na nuna aniyar samar da kyakkyawar makoma ga jihar.
A cewarsa, sabuwar tafiyar ADC na zuwa ne da manufar samar da shugabanci mai adalci, kyakkyawan mulki da manufofin da za su amfani al’umma kafin zaben gwamna na 2027.
“Ina matukar godiya ga Mai Girma Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da sauran shugabanni, matasa, mata da dukkan magoya baya bisa amincewar da suka nuna mini,” in ji Dan’iya.
Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar da su cigaba da kasancewa cikin lumana da hadin kai yayin da shirye-shiryen siyasa ke kara daukar zafi gabanin babban zaben kasa mai zuwa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sama da mutane 10 ne suka nuna sha’awar neman tikitin gwamna a jam’iyyar ADC a jihar Sokoto, ciki har da tsohon jakadan Nijeriya a Jordan, Faruk Malami Yabo.
