Jam’iyyar APGA ta yi watsi da hujjar da masu goyon bayan madugun adawa Atiku Abubakar ke yi na cewa ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu ba zai iya kayar da shugaban ƙasa mai ci daga yankin kudu ba a zaɓen 2027.
Masu goyon bayan Atiku sun bayyana cewa idan har jam’iyyar APC mai mulki ta ci gaba da tsayawa takarar shugaban ƙasa daga Kudu tare da Bola Ahmed Tinubu, to bai dace jam’iyyun adawa su ma su fito da ɗan takara daga yankin Kudun ba.
Sun ce tarihin siyasar Najeriya bai taɓa nuna inda ɗan takarar adawa daga yanki ɗaya ya kayar da shugaban ƙasa mai ci daga yankin nasa ba.
A cikin bayanin ‘yan gani kashenin Atiku sun kuma yi zargin cewa zuwa shekarar 2027 yankin Kudu zai kasance ya mulki Najeriya na kusan shekara 18 tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, yayin da ‘yan arewa suka yi mulkin shekaru 10 kacal.
Sun ce idan aka bar kudu ta sake yin wasu shekaru huɗu, gibi zai ƙara faɗaɗa, lamarin da suka ce bai dace da adalci ba.
Sai dai a martanin da ya yi wa jaridar PUNCH, Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APGA, Ejimofor Opara, ya ce kamata ya yi a bar yankin Kudu ya kammala zangonsa.
Ya ce duk wani ɗan arewa mai kishin ƙasa ya kamata ya mara wa wannan ra’ayi baya.
Opara ya kuma ce duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu da zai yi alƙawarin yin wa’adi guda na shekara huɗu ya fi dacewa da wanda zai nemi wa’adi biyu.
Ya ƙara da cewa haɗakar jam’iyyun adawa ta koma baya, tare da hasashen cewa kuri’un Tinubu za su ƙaru sosai a zaɓen 2027, yana mai cewa shugaban ƙasar ba zai rasa jihar Legas ba a wannan karon.
