DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, May 16, 2026
HomeLabaraiBabu ribar da muka samu na taimakon Buhari a zaben 2015 in...

Babu ribar da muka samu na taimakon Buhari a zaben 2015 in ji Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa Najeriya ta kai wani mataki da ake bukatar sauyi na gaskiya a shugabanci.

Kwankwaso ya yi zargin cewa matsalolin gwamnatocin da suka gabata ne suka haifar da wannan bukata a tsakanin al’umma.

Tsohon gwamnan Kanon ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin da kasar ke ciki tun daga dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

Ya ce tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya yi iya kokarinsa wajen tafiyar da kasa, amma marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya fuskanci matsalolin rashin lafiya a lokacin mulkinsa.

Haka kuma ya ce mulkin Goodluck Jonathan ya gamu da rikice-rikicen siyasa sakamakon yarjejeniyar wa’adin mulki guda daya da ake cewa an cimma.

Da yake magana kan gwamnatin yanzu, Kwankwaso ya ce “kowa ya san akwai matsaloli a wannan gwamnati,” yana nufin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya kara da cewa mutane a matakin kasa da kuma shugabannin siyasa suna nuna bukatar ganin an samu canji a shugabanci.

A cewarsa, matsalolin shekarun baya ne suka janyo yadda jama’a ke tururuwar shiga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress bayan shi da Peter Obi sun shiga jam’iyyar a ranar 3 ga watan Mayu.

Madugun na Kwankwasiyya ya ce mutane suna bude ofisoshi na jam’iyyar a wurare daban-daban a fadin duniya, abin da ya nuna karuwar goyon baya ga tafiyar tasu.

Kwankwaso ya kuma bayyana cewa kwarewar da ya samu a siyasa ta nuna masa cewa kasancewar shugaban kasa daga yankinku ba ya nufin za a samu shugabanci nagari kai tsaye.

Wannan ne, a cewarsa, ya sa yake goyon bayan a mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC na shekarar 2027 zuwa Kudancin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata