DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeKetareMashigar Hormuz a bude take ga kasashen da muke kawance - Iran

Mashigar Hormuz a bude take ga kasashen da muke kawance – Iran

Kasar Iran ta bayyana cewa mashigar ruwa ta Hormuz a bude take ga jiragen ruwa daga kasashen da take kallon kawaye, tana mai cewa an takaita zirga-zirga ne kawai ga kasashen da take dauka a matsayin makiya.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar BRICS da aka gudanar a New Delhi na kasar India.

“Daga mahangar mu, mashigar Hormuz ba a rufe take ba, musamman ga kasashe kawaye. An takaita ta ne kawai ga makiyanmu,” in ji Araghchi.

Ya kuma bayyana yiwuwar sassauta wasu takunkumai da rundunar ruwan Iran ta kakaba kan zirga-zirga a mashigar idan har yakin da Amurka da Isra’ila suka fara da Iran ya zo karshe.

“Idan yakin ya kare, za mu tabbatar da samar da cikakken tsaro ga dukkan jiragen ruwa,” in ji shi.

Tun bayan barkewar yakin, rundunar sojin Iran ta karbe ikon kula da mashigar Hormuz wadda ke da muhimmanci wajen jigilar makamashi a duniya.

Rahotanni sun ce barazana, bincike da hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa sun rage zirga-zirga sosai a mashigar, lamarin da ya haddasa tashin farashin makamashi da mai a duniya.

Iran ta dage cewa ba ta rufe mashigar gaba daya ba, amma kamfanonin jiragen ruwa na bukatar tuntubar jami’an Iran kafin a ba su izinin wucewa ta wata hanya da ke kusa da gabar kasar.

Masana dokokin kasa da kasa sun ce kudaden da Iran ke karba daga jiragen ruwa domin ba su damar wucewa ya saba wa dokar zirga-zirgar ruwa ta duniya.

A nata bangaren, Amurka ta sanya takunkumin jiragen ruwa kan Iran tun watan Afrilu domin rage kudaden shigar man fetur na kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata