DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeKetareTrump ya ce ya cimma manyan Yarjeniyoyi Da Xi a China

Trump ya ce ya cimma manyan Yarjeniyoyi Da Xi a China

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya cimma “manyan yarjeniyoyin kasuwanci” tare da warware wasu matsaloli daban-daban yayin ganawarsa da shugaban kasar China Xi Jinping a Beijing.

Trump ya bayyana hakan ne bayan kammala taron koli tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa tattaunawar ta samar da ci gaba mai kyau duk da cewa ba a fitar da cikakken bayani kan yarjeniyoyin ba.

Ya ce China ta amince da taimakawa wajen bude mashigar ruwa ta Hormuz tare da sayen jiragen Boeing 200 daga Amurka da kuma karin man fetur da waken soya daga kasar.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen China ba ta tabbatar ko musanta ikirarin Trump ba lokacin da aka tambaye ta bayan taron.

Trump ya bayyana Xi a matsayin “babban jagora” da kuma “aboki,” yayin da Xi ya ce ziyarar ta zama wani muhimmin mataki wajen gina sabuwar alakar diflomasiyya mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

A bangaren rikicin Iran kuwa, Trump ya ce Xi ya nuna aniyar taimakawa wajen bude mashigar Hormuz da ke da muhimmanci ga jigilar makamashi a duniya.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta fitar da sanarwa tana kira da a tsagaita wuta na dindindin a yankin tare da bude hanyoyin ruwa domin saukaka harkokin kasuwanci.

Trump ya kuma ce an tattauna batun kirkirar ka’idojin amfani da fasahar kirkirarriyar basira ta AI tsakanin kasashen biyu, yayin da shugaban Nvidia Jensen Huang ya halarci taron tare da tawagar ‘yan kasuwar Amurka.

Sai dai babu wata sanarwa kan takunkumin da Amurka ta sanya wa China na sayen manyan na’urorin AI masu ci gaba.

A yayin taron, Xi Jinping ya gargadi Amurka kan batun Taiwan, yana mai cewa duk wani kuskure kan lamarin na iya haddasa rikici tsakanin kasashen biyu.

Bayan kammala ganawar, Trump ya ce an samu ci gaba mai kyau duk da cewa har yanzu akwai sauran bambance-bambancen ra’ayi tsakanin Washington da Beijing.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata