DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeSiyasaCi-gaba da tsare El-Rufa'i rashin adalci ne - Atiku Abubakar

Ci-gaba da tsare El-Rufa’i rashin adalci ne – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna su gaggauta sakin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kafin bikin sallar layya.

Atiku ya bayyana ci-gaba da tsare El-Rufai a matsayin abin da ya saba wa adalci, dimokuradiyya da dokokin kasa, yana mai cewa hakan na tayar da zargin tsangwama ta siyasa.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce babu hujjar hana El-Rufai kasancewa tare da iyalansa a irin wannan lokaci na Sallah mai muhimmanci ga Musulmi.

Ya ce lokacin Eid-el-Kabir lokaci ne na tausayi, yafiya da hadin kai, saboda haka bai dace gwamnati ta yi amfani da karfin hukuma wajen tauye hakkin wani dan kasa ba tare da cikakken adalci ba.

“Atiku ya ce ci gaba da tsare El-Rufai ba tare da bayyana cikakken tsarin shari’a ba na iya kara jefa shakku kan yadda ake gudanar da mulki da bin doka a kasar nan.”

Jaridar Punch ta ruwaito tsohon mataimakin shugaban kasar ya gargadi gwamnati da kada ta yi amfani da hukumomin kasa wajen tsoratar da wadanda ake gani a matsayin abokan hamayya a siyasa.

Ya kara da cewa duk da bambancin siyasa, El-Rufai na da cikakken hakkin samun kariya karkashin kundin tsarin mulkin Nijeriya, ciki har da ‘yancin walwala da adalci.

Atiku ya ce dimokuradiyya mai kyau ana auna ta ne da yadda gwamnati ke mu’amala da masu adawa da ita ba kawai magoya bayanta ba.

Bukatar tasa na zuwa ne bayan hukumar ICPC ta sanar cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta bai wa El-Rufai damar samun kulawar lafiya yayin da yake tsare.

Ana tuhumar tsohon gwamnan tare da Joel Adoga kan zargin almundahanar kudi da mallakar kudaden da ake zargin an samo su ta hanyar cin hanci, zargin da suka musanta a gaban kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata