GRundunar ’yan sandan Abuja ta fara aiwatar da dokar hana amfani da motoci masu bakin gilashi “tinted” tare da kama fiye da motoci 30 da aka samu suna karya dokokin hanya a Abuja.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Kwamishinan ’yan sandan Abuja, CP Ahmed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, inda ya ce matakin na da nufin dakile laifukan da ake aikatawa da irin wadannan motoci.
Ya ce bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa masu aikata laifuka irin su satar mutane, fashin da ake yi na “one chance” da sauran miyagun laifuka suna amfani da motoci masu bakin gilashi da kuma lambobin mota da aka rufe domin ɓoye bayanansu da kauce wa jami’an tsaro.
A cewarsa, Sufeto Janar na ’yan sanda, Olatunji Disu, ya ba rundunar izinin fara aiwatar da dokar tare da tsaurara matakan ladabtar da masu karya ta.
Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta kaddamar da wani gagarumin samame kan motocin da ke amfani da bakin gilashi, lambobin mota da aka rufe ko kuma marasa cikakkiyar rajista.
Ya kara da cewa an riga an kwace motoci sama da 30 da aka samu sun karya dokokin, yayin da za a gurfanar da masu su a gaban kotu bisa tanade-tanaden dokokin tarayya da na harkokin sufuri na Abuja.
CP Sanusi ya jaddada cewa wannan mataki ba a yi don takura wa masu bin doka ba ne, sai dai domin hana masu laifi amfani da irin wadannan motoci wajen aikata laifuka ba tare da an gano su ba.
Ya kuma yi kira ga mazauna Abuja da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu da ya tayar musu da hankali domin inganta tsaro a babban birnin kasar.
