A cewar mai ba tsohon gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC na hana Malam Nasir El-Rufai samun kulawar likita duk da cewa yana fama da matsalar ido yayin da yake tsare a hannunta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi a wata sanarwa cewa El-Rufai ya nemi a kai shi asibiti domin a duba lafiyar idanunsa bayan sun fara kumbura, tare da ƙaiƙayi, amma jami’an ICPC sun ƙi amincewa da buƙatar tasa.
Ya ce duk da cewa an kai tsohon gwamnan wani asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, yanayin idanunsa ya kara tabarbarewa cikin dare, lamarin da ya tayar da hankalin iyalansa.
A cewar Adekeye, iyalan El-Rufai sun sanar da jami’an ICPC halin da yake ciki tare da bukatar a ba shi damar ganin likita, amma ba a samar masa da kulawar lafiya ba.
Ya kuma zargi wani jami’i mai suna Henry da ya sanar da wani dan uwansa cewa El-Rufai bai bukaci ganin likita ba, zargin da ya kira da rashin tausayi karara.
Adekeye ya kara da cewa lauyoyin El-Rufai sun samu umarnin kotu da ke ba shi damar samun kulawar likitocinsa da kuma kulawar lafiya, amma ya zargi ICPC da ci gaba da tauye masa hakkokinsa duk da wannan umarni.
Ya jaddada cewa babu wata hukuma da ya kamata ta hana wanda ke tsare a hannunta samun kulawar lafiya, yana mai kira ga ICPC da ta mutunta hakkin wadanda take tsare da su tare da bin umarnin kotu.
A baya, iyalan El-Rufai sun zargi ICPC da hana likitansa na kashin kansa ganawa da shi bayan ya je hedikwatar hukumar domin tattauna sakamakon wasu gwaje-gwajen lafiya da aka yi masa.
Haka kuma, sun yi zargin cewa matar El-Rufai, Aichatou, ta kai masa abinci da yamma amma jami’an hukumar suka hana ta shiga, suna masu cewa ba a karɓar abinci bayan karfe 6:30 na yamma.
Sai dai ICPC ta musanta wadannan zarge-zarge da ake yi mata, tana mai cewa ba ta hana El-Rufai hakkokinsa ba yayin da yake tsare a hannunta.
