DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKetareMutum 49 sun mutu da ƙishirwa a hamadar Nijar bayan lalacewar mota

Mutum 49 sun mutu da ƙishirwa a hamadar Nijar bayan lalacewar mota

Akalla mutum 49 sun rasa rayukansu sakamakon ƙishirwa a wani yanki mai nisa na hamadar Sahara a ƙasar Nijar bayan motar da ke ɗauke da su ta lalace a hanya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mamatan na cikin wata tawaga ce da ke dawowa daga ƙasar Mali domin halartar bukukuwan Sallah lokacin da suka rasa ruwa a tsakiyar hamada.

Gwamnatin yankin Agadez ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta bayyana cewa mutanen sun mutu ne a wani yanki da ke sama da kilomita 80 yamma da garin Assamaka, kusa da iyakokin Nijar da Aljeriya.

A cewar mahukuntan yankin, matafiyan sun makale ne bayan motar da ke jigilar su ta lalace, kuma duk ƙoƙarin da direba da fasinjojin suka yi na gyara ta bai yi nasara ba, rashin ruwa da tsananin zafin rana suka jefa su cikin mawuyacin hali har suka rasa rayukansu.

Sai dai mutum biyu sun tsira daga cikin tawagar bayan sun yi tafiyar sama da kilomita 50 a ƙafa zuwa wani wurin ruwa, kafin daga bisani su isa Assamaka inda suka sanar da hukumomi abin da ya faru.

Mahukunta sun ce an binne gawarwakin mamatan a kaburbura, yayin da aka ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Hamadar da lamarin ya faru ta kasance daya daga cikin manyan hanyoyin da bakin haure daga kasashen Afirka ke bi domin isa Turai, inda dubban mutane suka rasa rayukansu a tsawon shekaru sakamakon ƙishirwa, yunwa da tsananin yanayin hamada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata