Jam’iyyar PDP reshen Jihar Gombe ta zargi gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da bai wa wani mawaƙi daga Kano kyautar kuɗi da kadarori da darajarsu ta kai Naira miliyan 315.
A cewar jam’iyyar, an kashe Naira miliyan 115 wajen sayen motar kirar Coaster tare da ba shi Naira miliyan 200 a matsayin tallafi, sannan aka ware masa filaye huɗu a yankin Shehu Abubakar District Layout.
Jaridar Daily Trust ta ambato PDP ta ce ya kamata a karkata irin waɗannan kuɗaɗe zuwa fannin ilimi, lafiya, noma da ƙarfafa matasa, musamman ganin yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Sa’annan jam’iyyar ta buƙaci gwamnatin jihar ta bayyana dalilin wannan rabon kadarorin jama’a.
Sai dai Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa ƙage ne marasa tushe da PDP ke yi domin neman jan hankali yayin da ake tunkarar shekarar zaɓe ta 2027.
