DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaGwamnonin APC da ke neman wa'adi na biyu sun yi wata ganawa...

Gwamnonin APC da ke neman wa’adi na biyu sun yi wata ganawa a Kebbi

Gwamnonin APC a Nijeriya da ke neman wa’adi na biyu sun gudanar da wani taron sirri a Fadar Gwamnatin Jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi.

Rahoton jaridar Punch ya ce taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan ƙasa da kuma manufofin jam’iyyar.

Daga cikin gwamnonin da suka halarta akwai na jihohin Kaduna, Plateau, Ekiti, Delta, Zamfara, Kano, Jigawa, Ebonyi, Edo, Ondo, Kogi, Sokoto da Benue, yayin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, suka tarbe su.

Mai taimaka wa Gwamnan Kebbi kan Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai, Abuzaidu Yari, ya bayyana cewa taron zai karkata ne kan tattauna batutuwan ci gaban ƙasa, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, inganta shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ana sa ran shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC zai yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron bayan kammala zaman na yau.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata