Zaman Majalisar Wakilai ya rikide zuwa hayaniya a ranar Laraba bayan muhawara kan kudirin da ke neman a gayyaci Shugaba Bola Tinubu domin ya yi bayani kan zargin rashin sakin kuɗaɗen ayyukan mazabu.
Jaridar Punch ta ruwaito Ɗan majalisar Alex Mascot Ikwechegh ne ya gabatar da kudirin, inda wani ɗan majalisa ya kuma ba da shawarar dakatar da zaman majalisar na mako guda har sai an warware matsalar.
Sai dai Hon. Yusuf Adamu Gagdi daga jihar Filato ya yi adawa da kudirin, yana mai cewa aiwatar da ayyukan mazabu da sakin kuɗinsu nauyin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ne, ba shugaban ƙasa kai tsaye ba.
Rikicin ya sa Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya shiga tsakani, kafin daga bisani ya yi fatali da batun gayyatar shugaban ƙasa, yana cewa ba ya cikin ainihin kudirin da aka gabatar tun da fari.
