DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaKada ku tsaya jiran umarni kafin ku far wa 'yan ta'adda –...

Kada ku tsaya jiran umarni kafin ku far wa ‘yan ta’adda – Ministan Tsaron Nijeriya

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya umarci jami’an tsaro da kada su yi jinkirin ɗaukar mataki kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda idan aka tura su aiki.

Jaridar Punch ta ruwaito ya ce duk jami’in da ya ƙi farmakar ɗan ta’adda da hujjar jiran umarni, za a ɗauke shi tamkar mai haɗin gwiwa da masu aikata laifin.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jihar Sakkwato yayin ƙaddamar da motocin aikin tsaro guda 62 da sauran kayan aiki na tsaro da gwamnatin jihar ta saya kan kuɗi Naira biliyan 27.127 domin ƙarfafa yaƙi da ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Ya yabawa Gwamna Ahmad Aliyu bisa ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da motocin sulke, kayan leƙen asiri da sauran kayayyakin aiki, yana mai cewa hakan zai ƙara inganta motsi, tattara bayanan sirri da kare jami’an tsaro yayin gudanar da ayyukansu.

Sai dai Ministan ya gargadi jami’an tsaron da su kula da sabbin kayan aikin yadda ya kamata, tare da jaddada cewa dole su kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da cin zarafi ko muzgunawa fararen hula ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata