DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaA tarihin Nijeriya tsaro da tattalin arziki ba su taɓa muni haka...

A tarihin Nijeriya tsaro da tattalin arziki ba su taɓa muni haka ba – Dele Momodu

Fitaccen ɗan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kasa nuna nadama kan matsin tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke ciki.

Jaridar Punch ta ruwaito shi a wata hira da ya yi da ɗan jarida Rufai Oseni, Momodu ya ce halin ƙuncin rayuwa ya kai matsayin da yake jin tsoron buɗe saƙonnin wayarsa saboda yawan mutanen da ke neman taimakon kuɗi a wajensa.

Ya ce duk da cewa ya shaida ƙalubale daban-daban a Nijeriya tsawon rayuwarsa, bai taɓa ganin irin halin da ƙasar ke ciki a yanzu ba.

Haka kuma ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta yi muni fiye da kowane lokaci, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da cewa tana ɗaukar matakai ba tare da nuna cikakkiyar nadama kan halin da jama’a ke ciki ba.

Momodu ya kuma soki yadda shugaban ƙasa ke mu’amala da jama’a ta fuskar sadarwa, yana cewa shugaba ya kamata ya riƙa yi wa al’umma bayani akai-akai kan abubuwan da gwamnati ke yi.

Ya ƙara da cewa idan shi ne shugaban ƙasa, zai mayar da sadarwa da jama’a a matsayin babban ginshiƙin shugabanci da gwamnatinsa za ta fi bai wa fifiko.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata