DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeNishadiIna hidimar kuɗi kamar mai rariyar hannu, shi ya sa matata ke...

Ina hidimar kuɗi kamar mai rariyar hannu, shi ya sa matata ke kula da dukiyata — Davido

Fitaccen mawaƙin Afrobeats na Nijeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa matarsa, Chioma Adeleke, ce ke kula da harkokin kuɗinsa saboda shi mutum ne mai yawan kashe kuɗi ba tare da ƙa’ida ba.

Mawaƙin ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ya kira matarsa ta waya bayan ya kasa shiga asusunsa domin aika wa mataimakinsa, Lati, kuɗi.

Davido ya roƙi matarsa da ta tura wa mataimakinsa dala 4,000 a madadinsa.

A cikin hirar ta wayar, mawaƙin ya ce: “Sannu, sannu masoyiyata, barka da safiya. Don Allah ki taimaka ki aika wa Lati dala 4,000. Ban iya shiga asusuna ba, ban san dalili ba, watakila saboda network ɗin da ke nan.”

Bayan haka, wani mai watsa shirye-shiryen intanet, Davreltv, ya tambayi Davido ko matarsa ta karɓi ragamar kula da kuɗinsa.

Davido ya bayyana cewa “Tabbas, kun san ni mutum ne mai yawan kashe kuɗi, ita ce ke tsara komai, ita ce mai kula da rayuwata.”

Mawaƙin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yadda matarsa ke taimaka masa wajen tafiyar da harkokin kuɗinsa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsa.

A wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, an ga Davido yana kiran Chioma ne yayin da yake shirin tafiya Nijeriya.

Davido da Chioma Adeleke sun kasance cikin shahararrun ma’auratan da ake yawan magana a kansu a masana’antar waka ta Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata