Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara duba wani kudirin doka da zai tilasta wa manyan kamfanonin kafafen sada zumunta da ke gudanar da ayyukansuNijeriya kafa ofisoshin a cikin kasar.
An gabatar da kudirin ne a yayin wani taron sauraron ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisar dattawa mai kula da fasahar sadarwa da tsaron yanar gizo ya shirya a Abuja.
Kudirin, wanda Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa ya dauki nauyi, na neman yin garambawul ga dokar kare bayanan Nijeriya ta shekarar 2023, domin wajabta wa kamfanonin sada zumunta da ke aiki a Nijeriya kafa ofisoshi a cikin kasar.
Jaridar Punch ta ruwaito Sanata Nwoko ya ce manufar kudirin ba ita ce hukunta kamfanonin fasaha ko hana zuba jari ba, sai dai kara musu alhaki da kuma karfafa alakar su da Nijeriya.
Ya bayyana cewa kafa ofisoshin kamfanonin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, kara kudaden haraji, bunkasa kirkire-kirkire da kuma saukaka hulda tsakanin kamfanonin da hukumomin Nijeriya.
A nasa bangaren, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wanda mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Lola Ashiru, ya wakilta, ya ce kudirin ba na dakile ayyukan kamfanonin sada zumunta ba ne, illa dai domin tabbatar da karin alhaki da kyakkyawar mu’amala da kasar.
Haka kuma, taron ya samu goyon baya ga wani kudirin kafa cibiyar koyar da ilimin basirar na’ura mai kwakwalwa (Artificial Intelligence Academy) a Omuo-Ekiti, jihar Ekiti, wanda Sanata Yemi Adaramodu ya dauki nauyi.
Kwamitin majalisar dattawan ya ce zai duba bayanan da masu ruwa da tsaki suka gabatar kafin ya mika rahotonsa ga majalisar domin daukar matakin doka na gaba.
