DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeSiyasaJami'an Birtaniya a Nijeriya sun gana da ɓangaren PDP na Turaki

Jami’an Birtaniya a Nijeriya sun gana da ɓangaren PDP na Turaki

Ofishin Jakadancin Birtaniya a Nijeriya ya gana da ɓangaren jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki a Abuja, inda suka tattauna kan halin da dimokuraɗiyyar Nijeriya ke ciki da kuma rawar da jam’iyyun adawa ke takawa.

Tawagar ofishin jakadancin Birtaniya ta samu jagorancin Dr. Fortune Aldred, babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa, tare da Stephen Asek, mai ba da shawara kan siyasa mai kula da Kamaru.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren yaɗa labarai na ɓangaren PDP, Comrade Ini Ememobong, ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan halin dimokuraɗiyyar Nijeriya, matsayar jam’iyyun adawa, rikicin shugabanci da ke addabar PDP, da kuma batun yiwuwar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tsaya takara a zaɓen 2027.

A cewar Ememobong, shugaban ɓangaren PDP, Kabiru Tanimu Turaki, ya jaddada cewa kare tsarin jam’iyyu da tabbatar da wanzuwar jam’iyyun adawa na da matuƙar muhimmanci ga dorewar dimokuraɗiyya.

Turaki ya kuma zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC da abin da ya kira ƙoƙarin mamaye fagen siyasa, yana mai cewa hakan na ƙara zafin siyasar ƙasar.

“Yanayin siyasar ƙasar ya kai matakin tashin hankali, kuma hakan ya samo asali ne daga matakai da gazawar gwamnatin APC, wadda ke ƙoƙarin mallake dukkan sassan ƙasar,” in ji Turaki.

Da yake mayar da martani, shugaban tawagar ofishin jakadancin Birtaniya, Dr. Fortune Aldred, ya gode wa shugabannin jam’iyyar bisa tattaunawar, yana mai cewa za su isar da batutuwan da aka tattauna ta hanyoyin diflomasiyya da aka tanada.

Ya kuma bayyana cewa duk da cewa Nijeriya ƙasa ce mai cin gashin kanta kuma harkokin siyasar cikin gida nata ne, ofishin na da alhakin bibiyar abubuwan da ke faruwa tare da kai rahoto ta hanyoyin diflomasiyya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata