DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeSiyasaJam’iyyar APC ta zargi Atiku da hannu a badakalar dala 500,000 na...

Jam’iyyar APC ta zargi Atiku da hannu a badakalar dala 500,000 na aikin Mambilla

Kwamatin  yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na ƙasa ya nemi ɗan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da ya janye daga takarar shugabancin Nijeriya a 2027, bisa zargin da ta danganta da wasu bayanai da suka fito daga shari’ar aikin samar da wutar lantarki na Mambilla a gaban kotun arbitreshan ta ICC da ke Paris.

A cikin wata sanarwa da kakakinta, Dele Alake, ya fitar a ranar 18 ga Satumba, 2026, APC ta zargi Atiku da fifita muradun kansa kan na ƙasa, tana mai cewa abubuwan da suka bayyana a shari’ar sun haifar da tambayoyi kan rawar da ya taka a batun kwangilar Mambilla.

Batun ya shafi dala 500,000 da Leno Adesanya, shugaban kamfanin Sunrise Power and Transmission Company, ya tura wa Jennifer Douglas, tsohuwar matar Atiku, a ranar 30 ga Janairu, 2003, ta wani kamfani mai suna China Castle Investments Limited, zuwa asusun Citibank da ke Amurka.

Adesanya ya shaida wa kotun cewa kuɗin wani cinikin canjin kuɗi ne da aka yi wa Atiku, kuma ba shi da alaƙa da aikin Mambilla.

Sai dai kotun arbitreshan ta ce ba a gabatar mata da wasu muhimman takardu da za su tabbatar da wannan bayani ba, ciki har da shaidar takardun kuɗi na Naira da aka yi amfani da shi wajen cinikin, ƙimar canjin kuɗin, umarnin Atiku ko mataimakansa, ko wata wasiƙa da ke bayyana manufar kasuwancin.

Kotun ta kuma lura da kusancin lokacin da aka tura dala 500,000 da lokacin da aka danganta da bayar da kwangilar aikin Mambilla ga Sunrise.

Rahotannin da suka fito daga hukuncin sun nuna cewa kuɗin an tura su ne ƙasa da watanni huɗu kafin a ce an bai wa Sunrise kwangilar Build-Operate-Transfer (BOT) ta aikin samar da wutar lantarki na Mambilla mai ƙarfin megawatt 3,960.

Duk da haka, kotun ba ta yanke hukuncin cewa Atiku ya karɓi cin hanci ko kuma ya yi amfani da mukaminsa kai tsaye wajen tabbatar da kwangilar ba, sai dai ta ce bayanan da aka gabatar sun kasa kawar da tambayoyi kan alaƙar kuɗin da rawar Atiku a aikin.

A gefe guda, gwamnatin Nijeriya ta samu nasara a shari’ar da Sunrise Power ta shigar, inda kamfanin ke neman dala miliyan 680 a matsayin diyya da ruwa, yayin da wata da’awa mai alaƙa da aikin Mambilla ta kai sama da dala biliyan 2.7. Kotun ICC ta yi watsi da da’awar Sunrise, sannan ta umarci kamfanin da Adesanya su mayar wa Nijeriya mafi yawan kuɗaɗen shari’ar da ƙasar ta kashe.

Jam’iyyar APC dai ta yi amfani da waɗannan bayanai wajen sabunta zarge-zargen da take yi wa Atiku, tana mai cewa batun ya ƙara nuna bukatar ya fice daga fafatawar neman shugabancin kasar.

Jam’iyyar ta kuma danganta Atiku da tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye, kan yadda aka tafiyar da yarjejeniyar Mambilla, tare da cewa jinkirin aikin ya hana Taraba da Nijeriya damar cin moriyar manyan fa’idodin tattalin arziƙin da take ganin aikin zai iya samarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata