Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, EFCC, ta ce ta kwato jimillar Naira tiriliyan 1.233 tsakanin 1 ga Oktoban 2023 zuwa 31 ga Yulin 2026, a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Ola Olukoyede.
Jaridar Punch ta ruwaito EFCC ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta yi bayanin ayyukan da ta gudanar cikin watanni 34 na wannan lokaci.
Hukumar ta ce a cikin wannan lokacin ta karɓi korafe-korafe 49,673, inda 39,615 daga cikinsu aka gudanar da bincike a kansu, yayin da aka shigar da kararraki 14,476 a gaban kotuna.
Ta ƙara da cewa binciken da aka gudanar ya haifar da samun hukunci a kan mutane 10,872, a wani mataki da hukumar ta ce yana daga cikin ƙoƙarinta na yaƙi da laifukan da suka shafi kuɗi.
A cewar EFCC, laifukan da take yaƙi da su sun haɗa da manyan laifukan hada-hadar kuɗi, laifukan yanar gizo, halatta kuɗaɗen haram, damfarar banki da kuma zamba da ta shafi tafiyar da tattalin arziki.
Hukumar ta ce bayan kowace lamba da ta bayyana akwai bincike da aka gudanar, hanyoyin kuɗi da aka gano da kuma dukiyar jama’a da aka kwato.
EFCC ta ce aikin yaƙi da laifukan tattalin arziki da na kuɗi zai ci gaba da gudana, tana mai cewa kwato kuɗaɗen da aka wawure da gurfanar da masu aikata laifukan na daga cikin muhimman ayyukanta.
