Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Gombe ta umarci jam’iyyar PDP ta sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Gombe.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Garry ya kalubalanci Pantami ne bayan da PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani yadda ya dace ba.
Pantami, wanda ya kasance ɗan takarar da ke neman tikitin APC, ya koma PDP ne bayan APC ta amince da Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan takararta na yarjejeniya.
Daga bisani Pantami ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewa a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.
Sai dai a hukuncin da ta yanke, kotun ta umarci PDP ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani bisa ka’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta bayar da wannan umarni ne kan yadda aka samu tikitin Pantami, yayin da ake jiran ƙarin bayanai kan cikakken hukuncin kotun.
