Ofishin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar yake ya tattaunawa kan haɗin gwiwar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Daraktan yaɗa manufofin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar Premium Times a ranar Juma’a.
Shaibu ya ce har yanzu ba za su iya tabbatar da rahotannin da ke cewa Atiku ya ƙi amincewa da shawarar da aka gabatar na tsayar da ɗan takarar adawa guda ɗaya ba.
Ya kuma ce babu wata yarjejeniya da aka tabbatar a kan tsayar da ɗan takara guda ko haɗin gwiwar jam’iyyun adawa idan zaɓen shugaban ƙasa ya kai ga zagaye na biyu.
A cewarsa, “kofar a buɗe take” ga tattaunawar da za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa, yayin da yake cewa ana binciken cikakkun bayanai kan shawarar da ƙungiyar G100 ta gabatar.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton Jaridar Punch da ya ce G100 na nazarin yiwuwar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa idan zaɓen 2027 ya kai zagaye na biyu, bayan ƙoƙarin samar da ɗan takara guda ya ci tura.
A watan Agusta, ne G100 ta shirya taron jam’iyyun adawa a Abuja, inda wakilan ADC, Allied Peoples Movement, NDC, wani ɓangare na PDP, PRP da SDP suka halarta.
Taron ya samar da kwamitoci da ƙungiyoyin aiki domin duba haɗin kan adawa, shirin gyare-gyaren ƙasa da yiwuwar tsayar da ɗan takara guda.
