DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 3, 2026
HomeSiyasaAkpabio ya ce hadin kan majalisa da gwamnatin Tinubu na amfanar 'yan...

Akpabio ya ce hadin kan majalisa da gwamnatin Tinubu na amfanar ‘yan Najeriya

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya ce majalisar ƙasar za ta ci gaba da haɗa gwiwa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa hakan na cikin abin da ya dace da muradun ’yan Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da ya jagoranci tawagar ’yan majalisar ƙasa zuwa Legas domin ziyartar Shugaba Tinubu a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Akpabio ya ce majalisa ba ta ɗaukar aikinta a matsayin wanda ya saɓa wa shugaban ƙasa kawai, sai dai ta kasance abokiyar hulɗa da bangaren zartarwa wajen aiwatar da manufofin da suka shafi ƙasa. Ya ce wannan matsaya ba ta nufin Majalisar ta yi watsi da aikinta na sa ido kan gwamnatin tarayya ba.

Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar bangarorin biyu ya taimaka wajen sake duba wasu dokokin ƙasar da suka tsufa, musamman a fannin haraji.

A cewarsa, Majalisar ta yi wa dokokin da suka shafi harajin stamp duty da sauran dokokin tattalin arziki gyare-gyare domin dacewa da halin da ake ciki yanzu.

Shugaban majalisar Dattawan ya ce majalisar ta zartar da manyan dokokin haraji guda huɗu cikin gaggawa, duk da cewa tun farko wasu sassa na ƙasar sun nuna damuwa kan tasirinsu.

Ya ce ’yan majalisar sun yi nazarin dokokin kafin amincewa da su, yana mai cewa manufarsu ita ce samar da tsarin da zai amfani ƙasar baki ɗaya.

Akpabio ya kuma kare saurin da Majalisar ke yi wajen tantancewa da tabbatar da waɗanda Shugaba Tinubu ke naɗawa zuwa mukamai, yana mai cewa hakan na daga cikin haɗin gwiwar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki.

Ya ce Majalisar za ta ci gaba da zurfafa wannan haɗin gwiwa, yana mai cewa an zaɓi ’yan majalisar ne domin su yi aiki tare da gwamnatin da suke ganin tana ƙoƙarin sauya yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Sai dai Premium Times ta ruwaito cewa masu sukar majalisar ƙasar, ciki har da wasu ’yan siyasa da ƙungiyoyin fararen hula, sun zarge ta da wuce gona da iri wajen shige wa gwamnatin Tinubu tamkar ‘yan amshin shata.

Kodayake shugabannin majalisar sun sha musanta wannan zargi, suna cewa suna gudanar da aikinsu ne bisa abin da suka yi imanin zai amfani ’yan Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata