DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 3, 2026
HomeSiyasaShekarunka 24 kan madafun iko, me ka samar wa mahaifarka? - Wike...

Shekarunka 24 kan madafun iko, me ka samar wa mahaifarka? – Wike ga Amaechi

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci al’ummar masarautar Evo da su bayyana wani gagarumin ci gaba ko tallafin siyasa da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya kawo musu duk da ya shafe shekaru 24 yana riƙe da manyan mukaman siyasa.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki na masarautar Evo a ƙaramar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers, inda ya ce salon siyasarsa ya fi mayar da hankali kan bunƙasa ƙwarewar jama’a, ƙarfafa su da kuma samar da sabbin shugabanni.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ya ce Amaechi ya kasance Kakakin Majalisar Dokokin jihar Rivers na tsawon shekaru takwas, gwamna na shekaru takwas sannan minista na wasu shekaru takwas, amma ya ƙalubalanci jama’ar yankin da su nuna wani muhimmin aiki da ya ce ya jawo wa Evo ko jihar Rivers a tsawon lokacin.

Wike ya ce shi ma, lokacin da yake ƙaramin ministan ilimi, yana iya lissafa ayyukan da ya jawo wa jihar Rivers da mutanensa, yana mai cewa shugabanci bai kamata ya kasance hanyar hana wasu samun damar kaiwa ga manyan mukamai ba.

Ya kuma ce ba daidai ba ne shugaba ya yi ƙoƙarin hana wasu ’yan yankinsa zama gwamnoni ko samun damar jagoranci saboda kawai shi ya taɓa riƙe irin wannan matsayi.

Ministan ya bayyana cewa ba shi da wata babbar manufa ta siyasa da ta rage masa, yana mai cewa ya taɓa zama gwamna kuma ya yi minista sau biyu, don haka abin da yake nema shi ne tsawon rai da damar ci gaba da yi wa al’ummarsa hidima.

Wike ya kuma jaddada cewa shugabanci mai ɗorewa shi ne wanda ke barin wasu shugabanni a baya domin su ci gaba da aikin da aka fara, yana mai gargadin cewa siyasar da ta dogara kan mutum ɗaya tana iya rugujewa bayan rasuwarsa.

A yayin taron, wasu shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya, ciki har da Eze Temple Ejekwu da shugaban Evo Assembly, Elder Peter Chinwo, sun tabbatar wa Wike da goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar da Rainbow Coalition ta amince da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata