Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya shawarci gwamnatin Nijeriya da kada ta dawo da tallafin man fetur, yana mai ba da shawarar a samar da tallafi na musamman ga gidaje da al’ummomin da tsadar makamashi ta fi shafa.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa IMF ta bayyana hakan ne yayin da ake ƙara samun kiraye-kirayen dawo da tallafin man fetur a Nijeriya, musamman gabanin zaɓen shekarar 2027.
Daraktan sashen kula da harkokin kuɗaɗen gwamnati na IMF, Rodrigo Valdés, ne ya bayyana wannan matsaya yayin wani taron manema labarai kan rahoton Fiscal Monitor a taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na 2026, wanda aka gudanar a Bangkok.
Valdés ya ce irin wannan tallafi na ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati, musamman a lokacin da kuɗin rance ke ƙara tsada.
Da aka tambaye shi yadda IMF ke ba da shawarar barin farashin makamashi ya bi yanayin kasuwa alhali hakan na iya ƙara tsadar sufuri da hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, ya ce kare jama’a ba yana nufin dole ne gwamnati ta kare farashin man fetur ba.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen kare mutanen da tsadar makamashi ke jefa wa cikin mawuyacin hali, maimakon kashe kuɗaɗe wajen rage farashin mai ga kowa.
Valdés ya bayyana cewa a shekarar 2026, tallafin makamashi ko matakan da ke hana farashi bin sauye-sauyen kasuwa sun jawo wa ƙasashe kashe kuɗi da ya kai tsakanin kashi ɗaya zuwa kashi 1.5 na jimillar kayayyaki da ayyukan da suke samarwa a shekara (GDP).
IMF ta ba da shawarar amfani da shirye-shiryen tallafa wa al’umma da bayanan gidaje domin gano mutanen da suka fi buƙatar taimakon gwamnati.
Wannan hanya, a cewar asusun, za ta taimaka wajen tabbatar da cewa tallafi ya isa ga masu ƙaramin ƙarfi da sauran waɗanda tsadar rayuwa ta fi shafa.
A wani mataki na rage raɗaɗin tashin farashin man fetur, gwamnatin tarayya ta sanar da rangwamen farashin fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen sayar da man kamfanin NNPC Limited, inda aka ba masu safarar jama’a fifiko.
Sai dai shawarar IMF ta nuna cewa ya kamata gwamnati ta yi la’akari da hanyoyin tallafa wa jama’a kai tsaye, maimakon dawo da tallafin man fetur na bai ɗaya.
