Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira da a sake duba dokar kula da kudin haya ta jihar, domin kare ’yan haya daga karin kudin haya ba bisa ka’ida ba a gidaje da shaguna.
Shugaban Majalisar, Isma’il Falgore ya nuna bukatar hakan yayin zaman majalisar, bayan wani kudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Takai, Musa Kachako ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan yadda kudin haya ke ci gaba da tashi a fadin jihar.
Musa Kachako ya bayyana cewa, wasu masu gidaje sun kara kudin hayar shekara daga Naira 100,000 zuwa tsakanin Naira 200,000 da Naira 300,000, yayin da kudin hayar shaguna ya tashi daga Naira miliyan daya zuwa Naira miliyan biyu cikin shekara guda.
Ya ce wannan karin na kara jefa ’yan kasuwa, manoma da masu karamin karfi cikin matsin tattalin arziki, ganin yadda suke dogaro da gidajen haya da wuraren kasuwanci domin gudanar da rayuwarsu da samun abin dogaro.
Dan majalisar ya amince cewa, masu gidaje na da hakkin samun riba mai ma’ana daga jarin da suka zuba, amma ya bukaci a samar da dokokin da za su tabbatar da adalci wajen kara kudin haya, tare da hana yin karin kwatsam ba tare da isasshen sanarwa ba.
Ya kara da cewa, sake duba dokar da ake da ita zai taimaka wajen kare ’yan haya tare da tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin masu gidaje da wadanda suke haya.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tashin kudin hayar gidaje da shaguna a Kano, lamarin da ke kara nauyin kashe kudi ga mazauna jihar da kananan ’yan kasuwa.
