DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 13, 2026
HomeLabaraiKotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan bukatar gyara karar da...

Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan bukatar gyara karar da ke ƙalubalantar cancantar Tinubu a zaben 2027

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 20 ga Nuwamba domin yanke hukunci kan bukatar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na gyara ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar cancantar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC ta shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku da jam’iyyarsa ta ADC sun shigar da ƙarar ne a watan Agustan 2026, inda suka nemi kotun ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen saboda zargin cewa an miƙa wa hukumar zaɓen Nijeriya INEC takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC ta shugaban ƙasar da suka ce ta bogi ce.

Sai dai Tinubu da APC sun ƙalubalanci bukatar gyaran ƙarar, suka ce amincewa da ita zai zama kamar maye gurbin tsohuwar ƙarar da wata sabuwa, abin da suka ce doka ba ta yarda da shi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Alƙali Inyang Ekwo ne ya sanya ranar 20 ga Nuwamba domin yanke hukunci kan ko zai amince da gyaran ƙarar ko al’adun haka, bayan lauyoyin ɓangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu a zaman kotun na ranar Talata.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, Atiku da ADC sun nemi kotun ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairun 2027, wanda zai gudana tare da zaɓen ‘yan majalisun tarayya a faɗin ƙasar.

Sun kuma buƙaci kotun ta umarci INEC ta cire sunayen Tinubu da APC daga jerin ‘yan takara da jam’iyyun da za su fafata a zaɓen.

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan Atiku da ADC, Joseph Silas, ya buƙaci kotun ta amince da takardar neman gyaran ƙarar da ya shigar a ranar 10 ga Satumba.

Sai dai lauyan Tinubu, Wole Olanipekun SAN, ya yi amfani da wasu takardu da bukatar da ya shigar a ranar 24 ga Satumba, tare da ƙārin wasu takardun shari’a domin ƙalubalantar neman gyaran ƙarar.

Olanipekun ya buƙaci kotun ta yi watsi da bukatar, tare da cewa lokaci ya ƙure bisa tanadin doka, sannan ya jaddada cewa abin da masu ƙarar ke son yi ya wuce gyara ƙara, domin a zahiri suna ƙoƙarin shigar da sabuwar ƙara ne.

Yanzu haka dai ana jiran hukuncin kotun kan wannan buƙata, wanda zai fayyace ko Atiku da ADC za su samu damar gyara ƙarar tasu ko kuma za a ci gaba da shari’ar bisa yadda aka shigar da ita tun farko.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata