DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan majalisar wakilai 8 na LP da PDP sun sauya sheka a jihohin Delta da Enugu

-

A ranar Talata ‘yan majalisar wakilai takwas suka bayyana ficewa daga jam’iyyunsu zuwa wasu jam’iyyu daban-daban.

‘Yan majalisar wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, yayin da ‘yan majalisa biyu daga jihar Enugu suka bar jam’iyyar Labour suka koma PDP.

Google search engine

A yayin zaman majalisar na yau talata ne aka karanta sanarwar ficewar ‘yan majalisar.

Wadanda suka sauya sheka daga jihar Delta sun hada da Nicholas Mutu Bomadi da Nnamdi Ezechi, Jonathan Okodiko, Thomas Eriyetomi, Julius Pondi, da kuma Victor Nwokolo.

‘Yan jam’iyyar Labour da suka koma PDP sun hada da Mark Obetta daga Enugu da Dennis Agbo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijeriya ta zamo ta biyar a ƙasashen da suka fi ƙwarewa a harshen Turanci a nahiyar Afrika

A wani rahoto da EF SET na shekarar 2025 ta fitar kasar Afirka ta Kudu ce ta ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka wajen...

Majalisar Wakilan Nijeriya ta ɗage komawar zaman majalisa zuwa 5 ga Maris

Majalisar Wakilan Nijeriya, ta ɗage komawar zaman majalisa daga Talata, 24 ga Fabrairu 2026, zuwa Alhamis, 5 ga Maris 2026. Sakataren Majalisar, Kamoru Ogunlana, ya bayyana...

Mafi Shahara