Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMakarantu 7 ne kacal cikin 195 suka cika sharadin da ministan ilimin...

Makarantu 7 ne kacal cikin 195 suka cika sharadin da ministan ilimin Nijeriya ya gindaya- Cibiyar Athena

Bincike cibiyar Athena ta bayyana cewa, daga cikin manyan makarantun gaba da sakandire 195 na tarayya, guda bakwai ne kacal suka bi umarnin Ministan Ilimi na fitar da bayanan kudi da na dalibai, yayin da ya rage mako guda a cika wa’adin da aka gindaya.

Rahoton da Premiumtimes ta fitar ya ce daga cikin su, jami’ar Legas ce kadai ta yi fice wajen wallafa cikakkun bayanan kudadenta daga 2016 zuwa 2023.

Minista Tunji Alausa ya bukaci jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi su fitar da bayanai kan yawan dalibai, kudaden tallafi, harajin cikin gida da kudaden gwamnatin tarayya kafin 31 ga Mayu, a bayyane kuma cikin saukin fahimta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata