Jam’iyyar ADC ta bayyana kwanaki uku na zaman makoki ga mambobinta don girmama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a birnin Landan.
Sanarwar, wacce shugaban jam’iyyar na rikon ƙwarya, Sanata David Mark, ya fitar a Kano, ta bayyana Buhari a matsayin jagora wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasa – a matsayin soja da kuma shugaban farar hula.
David Mark ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da kammala manyan ayyukan raya ƙasa da Buhari ya fara, domin cigaba da amfani da su ga al’umma.
