Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya halarci zaman majalisar wakilan tarayya a ranar Talata domin shaida sauya shekar wasu ‘yan majalisar jam’iyyar PDP uku zuwa jam’iyyar APC.
Wadanda suka sauya sheka su ne Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da Sadiq Ango Abdullahi, kamar yadda Kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, ya sanar yayin zaman majalisar.
Kafin taron, majalisar ta dakatar da wasu ayyuka nata domin ba gwamnan damar halartar zaman, inda daga bisani ya jagoranci sabbin ‘yan jam’iyyar APC wajen gaisawa da kakakin majalisar da daukar hoto tare kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai jagoran ‘yan majalisar adawa, Kingsley Chinda, ya yi watsi da sauya shekar, inda ya bukaci kakakin majalisar da ya bayyana kujerunsu a matsayin babu mai rike da su bisa tanadin kundin tsarin mulki na kasa sashe na 68.