Gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba sabon takunkumi kan hukumar kula da mashigin ruwa na Strait of Hormuz ta Iran, wadda Tehran ta kafa domin karɓar kuɗaɗen zirga-zirgar jiragen ruwa da ke bi ta mashigin.
Kasar ta Amurka ce ta sanar da hakan ranar Laraba, inda ta zargi Iran da ƙoƙarin amfani da harkokin sufuri na ruwa wajen samun kuɗaɗe domin tallafa wa shirye-shiryen makamanta da ƙungiyoyin da Amurka ke kira masu tada ƙayar baya.
Ta ce matakin Iran na karɓar kuɗi daga jiragen ruwa masu wucewa ta mashigin Strait of Hormuz na nuna cewa takunkuman tattalin arzikin da aka sanya mata sun jefa gwamnatin cikin matsin kuɗi.
Amurka ta kuma yi barazanar cewa duk wata ƙasa ko kamfani da ya biya waɗannan kuɗaɗe na iya fuskantar takunkumi, saboda hakan na iya zama taimako ga Iran.
Mashigin Strait of Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, inda kusan kaso 25 cikin 100 na man fetur da iskar gas ke ratsawa ta wannan hanya.
A wani saƙo da hukumar kula da mashigin ta wallafa a shafin X ranar 20 ga watan Mayu, ta nuna taswirar yankin da ta ce yana ƙarƙashin ikon ta, tare da bayyana cewa dole ne jiragen ruwa su samu izinin Iran kafin su wuce.
Rahoton ya ce duk da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran tun ranar 8 ga watan Afrilu, har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a yankin yayin da tattaunawar diflomasiyya ke ci gaba da gudana.
