DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, October 4, 2026
HomeSiyasaAPC ta caccaki Amaechi kan ikirarin rashin kuɗin maganin mahaifiyarsa

APC ta caccaki Amaechi kan ikirarin rashin kuɗin maganin mahaifiyarsa

Jam’iyyar APC ta caccaki ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, kan ikirarinsa cewa rashin kuɗin sayen magani ne ya hana shi kula da mahaifiyarsa da ta rasu kwanan nan.

APC ta ce tsohon Gwamnan Jihar Rivers ya shafe shekaru da dama yana cin moriyar muƙaman gwamnati, tana mai cewa bai kamata ya nemi kujerar mataimakin shugaban ƙasa a 2027 domin ci gaba da dogaro da dukiyar gwamnati ba.

Jaridar Punch ta ruwaito Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Felix Morka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Morka ya yi ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyar Amaechi, Dame Ezinne Mary Oduah Amaechi, sannan ya yi suka kan bayanin da Amaechi ya yi game da matsalar rashin kuɗin maganin mahaifiyarsa.

Jam’iyyar ta kuma yi ishara da cewa Amaechi ya riƙe muƙaman gwamnati daban-daban na tsawon shekaru, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Gwamnan Rivers na wa’adi biyu da Ministan Sufuri na wa’adi biyu.

APC ta ce abin da ta kira “ikrarin” Amaechi na cewa ya shiga cikin matsalar rashin kuɗi bayan barin gwamnati na daga cikin dalilan da take ganin bai dace da neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa ba.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa Amaechi na neman tikitin ADC ne domin komawa kan kujerar gwamnati da kuma ci gaba da dogaro da abin da ta kira dukiyar jama’a.

A cikin sanarwar, APC ta ce fadar shugaban ƙasa ba wurin da ya kamata Amaechi ya dogara da shi domin samun abin dogaro da kai ba.

Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television ranar Juma’a, Amaechi ya zargi manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙara tsananta halin da ake ciki a ƙasar.

Ya ce matsalar tattalin arzikin da manufofin gwamnatin Tinubu suka jawo, a ganinsa, ta sanya masa wahala wajen samun kuɗin sayen maganin mahaifiyarsa, wadda ta rasu bayan doguwar jinya.

Martanin APC ya ƙara zafafa musayar kalamai tsakanin jam’iyyar da Amaechi yayin da siyasar zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara ɗaukar hankali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata