DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 5, 2026
HomeSiyasa’Yansanda sun kama mutane 5 kan zargin lalata allunan tallata Tinubu da...

’Yansanda sun kama mutane 5 kan zargin lalata allunan tallata Tinubu da Abba a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutane biyar da ake zargi da lalata allunan talla da fastocin Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu ’yan siyasa a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan matakan tsaro da kuma aiwatar da dokar hana hawan doki a bainar jama’a a Kano.

Bakori ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan rundunar ta gudanar da bincike kan lalata kadarori a lokacin da ake fama da tashin hankali da ya biyo bayan batun hawan doki da jerin gwanon jama’a a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, rundunar ta kammala bincikenta, sannan an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar tuhumar da ake yi musu.

Kwamishinan ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda aka samu da aikata laifin da ka iya barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Kamen na zuwa ne bayan fitowar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce wasu daga cikin mutanen da suka raka shi sun lalata fastoci da allunan tallan Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa.

A cewar Kwamishinan ’Yan Sandan, lamarin ya ƙara tsananta yanayin da ake ciki a Kano, musamman ganin cewa ana ci gaba da samun takaddama kan masarautar Kano.

Batun takaddamar masarautar Kano ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da suka janyo ce-ce-ku-ce da rikicin siyasa da na masarauta a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan ta ce za ta ci gaba da tabbatar da bin doka da oda, tare da ɗaukar matakan da suka dace kan duk wani abu da zai iya janyo tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Kwamishinan ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ka iya haifar da rikici, musamman a lokacin gudanar da tarukan jama’a da jerin gwanon siyasa ko na masarauta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata