DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 5, 2026
HomeLabaraiJihohin Nijeriya sun karɓi N32bn yayin da ambaliya ke barazana a wasu...

Jihohin Nijeriya sun karɓi N32bn yayin da ambaliya ke barazana a wasu sassan kasar

Jihohin 36 na Nijeriya sun karɓi kusan N32bn daga asusun kula da muhalli a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026, yayin da ake ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Binciken jaridar Punch ya nuna cewa wasu jihohi sun kashe kaɗan ko kuma ba su kashe komai ba wajen ayyukan magance ambaliya da zaizayar ƙasa, yayin da wasu kuma ba su fitar da cikakken rahoton yadda suka kashe kuɗin ba.

Bayanan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya sun nuna cewa jihohin sun samu kuɗin ne tsakanin Janairu da Yuni 2026. An ware N4.69bn a Fabrairu, N5.01bn a Maris, N5.77bn a Afrilu da N5.38bn a Yuni.

Kano ce ta karɓi mafi yawa da kusan N1.91bn, sai Kaduna da N1.58bn, Jigawa N1.55bn, Borno N1.50bn da Katsina N1.48bn. Jihohi 10 da suka fi karɓar kuɗin sun samu sama da N15.5bn gaba ɗaya.

Sai dai bayanan kashe kuɗin sun nuna gibi tsakanin kuɗin da aka samu da ayyukan da aka aiwatar. A Jigawa, wadda ta karɓi kusan N1.55bn, gwamnatin jihar ba ta kashe komai kan ayyukan magance zaizayar ƙasa da ambaliya a rabin farko na shekarar ba, duk da cewa ta tanadi N100m a kasafinta.

A Kaduna kuma, jihar ta kashe N178m kacal kan ayyukan ambaliya da zaizayar ƙasa a wani lokaci da ta karɓi sama da N3bn daga asusun kula da muhalli a shekarar 2025. Bauchi, Niger da Benue kuwa ba su fitar da cikakkun rahotannin kashe kuɗin 2026 ba a lokacin da aka gudanar da binciken.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da Gwamnatin Nijeriya ta yi gargadin yiwuwar ambaliya a wasu jihohi 24 da Abuja tsakanin 27 ga Satumba zuwa 10 ga Oktoba. Kimanin al’ummomi 14,000 ne aka yi hasashen za su fuskanci ambaliya daban-daban.

Cibiyar National Flood Early Warning Systems ta sanya Benue, Kogi, Kwara, Niger, Adamawa, Bauchi, Taraba da wasu jihohin kudanci cikin rukunin wuraren da ke cikin babban haɗarin ambaliya. Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Borno da wasu jihohin Arewa kuma na cikin wuraren da aka sanya a jerin masu matsakaicin haɗari.

Masana muhalli sun nuna damuwa kan yadda ake amfani da Ecological Fund. Danjuma Dangwa ya ce rahotannin kasafin kuɗin jihohi ba sa bayyana yadda aka yi amfani da kuɗin, yayin da Philip Jakpor na Renevlyn Development Initiative ya nemi a gudanar da binciken musamman kan yadda aka raba da kuma amfani da kuɗin daga 2023 zuwa 2026.

Farfesa Abubakar Manga na Jami’ar Maiduguri shi ma ya ce duk da cewa jihohi da ƙananan hukumomi sun dade suna karɓar kuɗi daga sausun kula da muhalli, har yanzu yana da wahala a ga tasirin ayyukan da aka gudanar da kuɗin.

Yayin da barazanar ambaliya ke ci gaba, wasu jihohi sun fara ɗaukar matakan kariya. Wasu sun buƙaci mazauna yankunan da ke kusa da koguna da wuraren da ke fama da ambaliya su koma wuraren da suka fi tsaro, yayin da hukumomin agaji ke shirya matsugunai da sauran matakan gaggawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata