DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeSiyasaAPC ta danganta kayen da Atiku ya wa Tinubu a Kaduna a...

APC ta danganta kayen da Atiku ya wa Tinubu a Kaduna a 2023 da salon mulkin El-Rufai

Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta bayyana cewa rashin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hannun Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a jihar ya samo asali ne daga rashin gamsuwar jama’a da salon mulkin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren yaɗa labaran APC a Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan shirye-shiryen tarbar Shugaba Tinubu a jihar domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar na 2027.

Haruna ya zargi gwamnatin El-Rufai da rushe gidaje da kasuwanni, korar dubban ma’aikata da kuma amfani da bambance-bambancen addini da ƙabila wajen tafiyar da mulki.

A cewarsa, waɗannan manufofi sun jawo fushin wasu ɓangarorin al’umma, musamman a Kudancin Kaduna, inda masu zaɓe da dama suka nuna goyon baya ga jam’iyyun adawa a zaɓen 2023.

Ya ce zaɓen 2023 a Kaduna ya zama wata hanya da jama’a suka bayyana matsayarsu kan salon shugabancin gwamnatin wancan lokaci.

Haruna ya bayyana cewa yanayin siyasar jihar ya sauya tun bayan hawan gwamna Uba Sani kan mulki, yana mai cewa gwamnan ya rungumi salon mulkin da ya haɗa mutane daga addinai, ƙabilu da jam’iyyun siyasa daban-daban.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Uba Sani ta nuna girmamawa ga jama’a ba tare da la’akari da addininsu, ƙabilarsu, matsayinsu na tattalin arziki ko al’adunsu ba, lamarin da ya ce ya ƙara wa APC farin jini a jihar.

Mai magana da yawun jam’iyyar ya yi iƙirarin cewa APC a yanzu tana da rinjaye a dukkan muƙaman zaɓe a Kaduna, sabanin yadda lamarin yake kafin zaɓen 2023, lokacin da jam’iyyun adawa suka samu gagarumar nasara a wasu sassan jihar.

Haruna ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa APC za ta samu gagarumin goyon baya a zaɓen 2027, ciki har da samun nasarar sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Ya ce gwamna Uba Sani ya tabbatar wa shugaban ƙasar cewa jihar Kaduna za ta samar masa da ƙuri’u miliyan biyu a zaɓen mai zuwa.

A cewarsa, jam’iyyar na ganin wannan buri zai yiwu saboda salon shugabancin gwamnan da kuma yadda take ikirarin samun ƙarin goyon bayan jama’a.

Haruna ya kuma yi watsi da hasashen cewa jam’iyyun adawa za su iya maimaita irin nasarar da suka samu a Kaduna a zaɓen 2023, yana mai cewa halin da siyasar jihar take ciki a yanzu ya bambanta da wancan lokaci.

Ya bayyana cewa APC na shirin tattara dubban magoya baya domin tarbar Shugaba Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar da za su halarci ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata