Jam’iyyar APC ta dakatar da zaɓen fidda gwani na kujerar gwamnan jihar Kwara da aka shirya gudanarwa Alhamis din nan, lamarin da ya jefa jam’iyyar cikin sabon ruɗani da rikicin cikin gida gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an sanar da dakatar da zaɓen ne a daidai lokacin da magoya bayan jam’iyyar suka fara taruwa a rumfunan zaɓe daban-daban domin gudanar da zaɓen fidda gwani a faɗin jihar.
Matakin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan jam’iyyar ta sauya matsayarta kan dakatar da wasu masu neman takarar kujerun majalisar dokokin jihar Kwara, inda tun farko aka hana sama da mutum 100 shiga takara kafin daga baya a sake amincewa da su.
Rahotanni sun nuna cewa tsakanin mutum 105 zuwa 113 ne aka fara cirewa daga jerin masu neman tikitin majalisar dokokin jihar, lamarin da ya haifar da zarge-zarge da ce-ce-ku-ce a cikin APC.
Sai dai a ranar Laraba, jam’iyyar ta sake fitar da sabon jerin sunayen da ya nuna cewa dukkan masu neman takara 159 sun samu damar shiga zaɓen fidda gwani, ciki har da Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Yakubu Danladi-Salihu wanda tun farko ba a saka sunansa ba.
Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa dakatar da zaɓen fidda gwani na gwamna na da alaƙa da ƙoƙarin shugabannin jam’iyyar na rage zafin rikicin cikin gida da kuma sasanta masu ruwa da tsaki kafin gudanar da zaɓen.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na jihar Kwara, Abdulwaheed Olawale Babatunde ya fitar, ya ce an ɗage zaɓen daga ranar 21 ga watan Mayu zuwa ranar Juma’a 22 ga watan Mayu, 2026.
Abin mamaki kuwa shi ne, kafin sanarwar ta fito, Babatunde ya shaida wa Daily Trust cewa zaɓen zai gudana kamar yadda aka tsara, yana mai cewa babu wani ɗan takara da ya janye daga takara kuma duk masu neman kujerar gwamna 16 za su fafata.
Dakatar da zaɓen ba zato ba tsammani ya haddasa ruɗani a tsakanin magoya bayan jam’iyyar da suka taru a rumfunan zaɓe daban-daban, musamman ganin cewa an riga an fara shirye-shiryen jefa ƙuri’a da tattara magoya baya.
Shugaban APC na jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya tabbatar da cewa umarnin dakatar da zaɓen ya fito ne kai tsaye daga shugabancin jam’iyyar na ƙasa, yana mai cewa ba su samu cikakken bayani kan dalilin ɗage zaɓen ba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa an samu rade-radin cewa wasu daga cikin masu neman takara sun janye domin marawa Ambasada Yahaya Seriki baya, wanda ake ganin shi ne ɗan takarar da gwamnan jihar ke goyon baya.
A wasu rumfunan zaɓe kuwa, musamman a yankin Adewole Ward da ke Ilorin, dubban magoya bayan APC sun fito domin nuna goyon baya ga tsarin siyasar gwamnan jihar, yayin da wasu masu sa ido suka nuna damuwa kan rashin isasshen kulawa daga jami’an INEC.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da fuskantar rashin tabbas a cikin APC ta jihar Kwara shin ko za a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani ko kuma shugabannin jam’iyyar za su koma tsarin maslaha wajen zaɓen ɗan takara guda.
