DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiSoko ne kawai zai yarda Tinubu nake yi wa aiki - Kwankwaso

Soko ne kawai zai yarda Tinubu nake yi wa aiki – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da zargin cewa yana yi wa Tinubu aiki a boye domin taimaka masa wajen sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Global TV a daren Laraba, inda ya ce jita-jitar cewa yana mara wa Tinubu baya ba sabon abu ba ne, domin tun yana jam’iyyar NNPP ake yaɗa irin wannan zargi a kansa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zargin a wata hira da Arise TV cewa Kwankwaso na taimaka wa Tinubu a fakaice gabanin zaɓen 2027.

A cewar Sunusi Bature, akwai masu yi wa Tinubu aiki a fili, sannan akwai waɗanda ke taimaka masa a bayan fage, yana mai cewa duk abin da Kwankwaso ke yi a siyasa Tinubu ke amfanawa.

Ya kuma yi zargin cewa Kwankwaso ya taimaka wa Tinubu a zaɓen 2023, saboda haka yana ganin akwai yiwuwar hakan zai sake faruwa a 2027.

Sai dai da yake martani kan zargin, Kwankwaso ya ce mutum “Soko” ne kawai zai yarda da cewa yana yi wa Tinubu aiki a boye, yana mai jaddada cewa shi da magoya bayansa suna aiki ne domin nasarar jam’iyyar NDC kawai.

“Bola Tinubu babban yayana ne kuma abokina tun shekaru da dama, amma hakan ba yana nufin za mu haɗa manufofin siyasa tare ba, shi yana tafiyar da siyasarsa, ni kuma ina tafiyar da tawa,” in ji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan Kanon ya kuma ce shugaban ƙasa ba ya ganin yadda al’amura suke tafiya a ƙasa saboda mutanen da ke kewaye da shi ba sa gaya masa gaskiyar halin da ƙasa ke ciki.

A cewarsa, mafi yawan mutanen da ke kusa da Tinubu su ne ke haddasa matsalolin siyasar ƙasar, kuma sun fi mayar da hankali wajen jan gwamnoni zuwa APC maimakon magance matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Kwankwaso ya kuma kare matsayarsa na goyon bayan Peter Obi, inda ya ce bayan tattaunawa da shugabannin siyasa daga yankuna shida na ƙasar nan, sun yanke shawarar cewa Obi shi ne mafi dacewa daga Kudancin Nijeriya domin ya jagoranci tikitin shugaban ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata