DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiƊan majalisa a Kano mai rigar fata ya fice daga APC zuwa...

Ɗan majalisa a Kano mai rigar fata ya fice daga APC zuwa NDC

Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Gwale, Abdulmajid Mai Rigar Fata, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NDC bayan ya gaza samun tikitin sake tsayawa takara a zaɓen 2027 mai zuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an karɓi ɗan majalisar ne ranar Alhamis ta hannun tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Maitama a Abuja.

Abdulmajid Mai Rigar Fata yana wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, wadda ita ce mazaɓar gwamna Abba Kabir Yusuf a majalisar dokokin jihar Kano.

Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ne ya bayyana sauya shekar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.

A cewarsa, baya ga Abdulmajid Mai Rigar Fata, an kuma karɓi tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Kabiru Sani Auwal Obi, da Mahadi Isa Umar, waɗanda suma suka shiga jam’iyyar NDC tare da shi.

Rahotanni sun nuna cewa Abdulmajid ya shiga majalisar ne a shekarar 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP kafin daga bisani ya koma APC tare da gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sai dai ana zargin rashin samun tikitin komawa takara a APC ne ya sanya ɗan majalisar sauya sheƙa zuwa sabuwar jam’iyyar NDC.

Sauya shekar tasa na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan wata kotun tarayya ta ba ‘yan siyasa damar sauya jam’iyya zuwa wasu jam’iyyun domin shiga zaɓe ba tare da matsi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata