Shugaban hukumar da ake zargin ta bogi ce mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council, Prince Adeyemi Matthew Adeniyi, ya ce har yanzu bai san yadda aka yi aka saka sunan hukumar cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na shekarar 2026 ba.
A wata hira da ya yi da Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, Adeniyi ya bayyana cewa tun a watan Disamban 2024 ya kai buƙatar a saka hukumar cikin kasafin 2025, amma jami’an ofishin kasafin kuɗi suka shaida masa cewa an riga an kammala aikin kasafin shekarar.
Ya ce daga baya aka ba shi tabbacin cewa za a sake duba buƙatar ne yayin shirya kasafin kuɗin shekarar 2026.
A cewarsa, wata jami’a ce ta taimaka masa wajen ganawa da manyan jami’an ofishin kasafin kuɗi domin tattauna batun.
Sai dai Adeniyi ya musanta zargin cewa ya bai wa wani jami’i cin hanci don a saka hukumar cikin kasafin.
Ya ce abin da kawai ya yi alkawari shi ne samar da guraben aiki ga wasu idan har hukumar ta fara aiki.
Ya ƙara da cewa bayan kama shi da kuma fara shari’a a kansa, ya daina bibiyar batun gaba ɗaya.
Saboda haka ya ce, abin ya ba shi mamaki lokacin da ya ji cewa an saka sunan hukumar cikin kasafin kuɗin 2026.
Dangane da zargin cewa ya biya kuɗi da darajarsu ta kai kusan naira miliyan 400 domin samun mukaminsa, Adeniyi ya ce an ba wani marigayi mai suna Dolapo Tanimola kuɗin ne a dalar Amurka.
Haka kuma ya jaddada cewa bai taɓa haɗuwa kai tsaye da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ba.
A nasa ɓangaren, VeryDarkMan ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan Ofishin kasafin kuɗi da sauran hukumomin gwamnati domin gano yadda aka saka sunan hukumar cikin kasafin, yana mai cewa idan zarge-zargen Adeniyi suka tabbata, bai kamata shi kaɗai ya ɗauki alhakin lamarin ba.
