DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 28, 2026
HomeLabaraiFaɗan da ke tsakanin gwamnonin APC da Wike a dalilin kuɗi ne...

Faɗan da ke tsakanin gwamnonin APC da Wike a dalilin kuɗi ne – Sowore

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar AAC Omoyele Sowore, ya ce rikicin siyasar da ke tsakanin wasu gwamnonin APC da ministan Abuja Nyesom Wike, ya samo asali ne daga batun kuɗi da kuma yadda ake tafiyar da harkokin siyasa.

Sowore ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya yi tsokaci kan rikicin siyasar da ke ƙara bayyana tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC gabanin zaɓen 2027.

A cewarsa, rikicin ba wai kawai batun jam’iyya ko tsarin siyasa ba ne, sai dai yana da alaƙa da yadda ’yan siyasa ke neman samun iko da albarkatun da ke tattare da harkokin siyasa.

Sowore ya yi wannan ikirarin ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC kan ƙungiyar ‘Rainbow Coalition’ da ministan ke jagoranta.

Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne, yana cikin jam’iyyar PDP, amma yana aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wadda APC ke jagoranta.

A baya dai Wike ya bayyana cewa ‘Rainbow Coalition’ na da nufin goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ba tare da dole sai ’yan siyasar da ke cikin ƙungiyar sun koma APC ba.

Sai dai wasu gwamnonin APC sun nuna rashin amincewa da wannan tsarin, inda suka buƙaci Wike ya shiga APC a hukumance idan yana son yin aiki tare da jam’iyyar.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, na daga cikin waɗanda suka bayyana wannan matsaya, inda ya ce Wike ya kamata ya zaɓi ko dai ya kasance cikin APC ko kuma ya ci gaba da tafiya da Rainbow Coalition.

Wannan matsaya ta jawo muhawara kan ko zai yiwu ɗan siyasa ya goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na wata jam’iyya, yayin da a sauran matakan zaɓe yake goyon bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu.

Sai dai Sowore ya ɗauki batun daga wani bangare, inda ya ce abin da ke bayan rikicin shi ne fafatawa kan kuɗi, iko da tsarin siyasar ƙasar.

Ya kuma yi suka kan yadda manyan ’yan siyasa ke tafiyar da harkokin jam’iyyu da zaɓe, yana mai cewa bai kamata a bar batun siyasa ya ta’allaka kacokan kan neman iko da albarkatun ƙasa ba.

A halin yanzu, rikicin Wike da wasu shugabannin APC na ci gaba da jan hankalin masu bibiyar siyasar Nijeriya, musamman yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata