DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 28, 2026
HomeLabaraiWata mata ta rusa wa kishiyarta tabarya a jihar Bauchi

Wata mata ta rusa wa kishiyarta tabarya a jihar Bauchi

Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, bisa zargin halaka kishiyarta, Jamila Adamu, mai shekaru 43, a wani gida da ke Tafawa Balewa Housing Estate a cikin birnin Bauchi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana kama matar a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Bauchi.

A cewarsa lamarin ya faru ne a ranar 27 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 4:05 na yamma, bayan rundunar ’yan sanda ta C-Division da ke Bauchi ta samu sahihin bayani kan wata matsala ta cikin gida da ta taso tsakanin matan biyu da suke zaune a gida ɗaya.

SP Nafiu Habib ya ce binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Hauwa’u, wadda ita ce amarya, ta ɗauki taɓarya sannan ta bugi Jamila, wadda ita ce ta farko, a lokacin da ake zargin tana cikin wani yanayi na rashin fahimtar abin da ke faruwa.

Ya ce bayan samun rahoton, jami’an bincike na C-Division sun garzaya wurin da lamarin ya faru domin gudanar da binciken farko tare da rubuta bayanan abin da ya faru.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa an garzaya da Jamila zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi domin samun kulawar likitoci.

Sai dai likita ya tabbatar da cewa Jamila ta rasu, bayan haka aka kai gawarta ɗakin ajiye gawawwaki na asibitin domin gudanar da binciken gawar da ya dace.

A gefe guda kuma, ’yan sanda sun kama Hauwa’u, wadda ake zargi da hannu a lamarin, yayin da aka kwato tabaryar da ake zargin an yi amfani da ita a matsayin hujjar bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin tura lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.

Kwamishinan ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan marigayiyar tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da binciken lamarin domin gano cikakkun bayanai da suka kai ga faruwar mutuwar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata