Shugaban jam’iyyar APC a Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi kira ga duk masu neman tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar da su nuna cikakken ladabi, dattako da sanin ya kamata yayin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani na shekarar 2027 ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun bayanai ya fitar, shugaban APC ya yi wannan kira ne ga ’yan takarar da suka halarci tantancewar da kwamitocin jam’iyyar suka gudanar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Farfesa Yilwatda ya ce APC na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani cikin lumana da gaskiya domin ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida da kuma tabbatar da amincewar da ’yan Najeriya ke bai wa jam’iyyar mai mulki.
Ya gargaɗi cewa shugabancin jam’iyyar ba zai lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga gudanar da zaɓen ba.
Ya bayyana cewa duk wani ɗan takara ko magoya bayansa da aka samu da tayar da tarzoma, ɗaukar nauyin rikici, aikata ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya ko kuma yunƙurin lalata sahihancin tsarin zaɓen, zai fuskanci matakin ladabtarwa har da dakatarwa nan take.
A cewarsa, APC ta shafe lokaci tana gina suna a matsayin jam’iyyar siyasa mafi tsari a Najeriya, don haka ba za a bari wata buƙatar mutum ɗaya ta zarce muradin jam’iyyar da zaman lafiyar ƙasa ba.
Shugaban jam’iyyar ya kuma tunatar da masu neman takara cewa duk wata gasa ta siyasa tana da masu nasara da masu faɗuwa, yana mai cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar gasa mai tsafta da mutunta sakamako.
“A kowace gasa ta dimokuraɗiyya, mutum ɗaya ne kawai zai yi nasara. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda aka gudanar da tsarin cikin mutunci,” in ji shi.
Haka kuma, ya buƙaci duk masu neman takara da su ɗauki kansu a matsayin jakadun APC, yana mai cewa halayensu kafin, lokacin da bayan zaɓen fidda gwani za su nuna ƙimar jam’iyyar da manufofinta.
