DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, September 13, 2026
HomeSiyasaKuskure Peter Obi ya yi na zaɓar Kwankwaso a matsayin mataki -...

Kuskure Peter Obi ya yi na zaɓar Kwankwaso a matsayin mataki – Jam’iyyar NNPP

Jam’iyyar NNPP ta ce jam’iyyar NDC ta yi babban kuskure wajen zaɓar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya yi suka mai ƙarfi kan matakin da NDC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, suka ɗauka.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Olaposi ya ce a ra’ayinsu, zaɓen Kwankwaso a matsayin abokin takarar Obi na iya jefa NDC cikin matsala a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya bayyana matakin a matsayin “babban kuskure da kuma cin amanar mutane”, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta samu nasarar da take fata ba idan ta ci gaba da wannan tsari.

NNPP ta ce tana ganin haɗin kan Obi da Kwankwaso ba zai samar da sakamakon da magoya bayan NDC ke fata ba, musamman ganin irin bambance-bambancen siyasa da ke tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

A cewar Olaposi, NNPP na ganin cewa zaɓen abokin takara na ɗaya daga cikin muhimman matakan da ke iya tasiri kan damar ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe.

Ya ce abin da Obi da shugabannin NDC suka yi ya nuna rashin kyakkyawan tunani wajen tsara dabarun da za su taimaka musu wajen samun nasara a 2027.

NNPP ta kuma bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance gagarumar fafatawa tsakanin manyan jam’iyyun siyasa, don haka dole ne kowace jam’iyya ta yi taka-tsantsan wajen zaɓar mutanen da za su wakilce ta.

Sai dai har yanzu NDC da Peter Obi ba su mayar da martani kan wannan suka daga NNPP ba.

Sanarwar ta kuma nuna cewa NNPP na ci gaba da sukar tsarin siyasar da NDC ke bi yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ana sa ran batun zaɓen Peter Obi da Rabiu Kwankwaso zai ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jam’iyyun siyasa da magoya bayansu yayin da ake ƙara matsowa kusa da babban zaɓen ƙasar na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata