DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, September 13, 2026
HomeSiyasaYadda iyalan El-Rufa'i suka gargadi Ministan tsaron Nijeriya

Yadda iyalan El-Rufa’i suka gargadi Ministan tsaron Nijeriya

Gargadi mai ƙarfi Ga ministan tsaron Nijeriya Christopher Musa, na janye kalamsa cikin kwanaki bakwai ko mu hadu a kotu inji iyalan El-Rufa’i

A wata sanarwa da Hwanarabul Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan Malam Nasiru El-Rufai a Abuja Litinin din nan, sun ce sun damu matuƙa da zargin da Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi wa El-Rufa’i a ranar 3 ga Satumba, 2026, yayin wata hira kai tsaye a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Sun ce ministan bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da wannan zargi ba.

Iyalin El-Rufai sun ce duk da cewa Janar Musa mai ritaya ya na da damar bayyana ra’ayinsa, su ma suna da damar neman a tabbatar da irin wannan mummunan zargi da sahihan hujjoji.

Sun buƙaci Ministan tsaron na Nijeriya ya janye wannan mummunan zargi na cewa Mallam Nasir El-Rufai ya shirya kisan mutane a Kudancin Kaduna lokacin da yake Gwamnan Jihar.

Suna buƙatar ya fito bainar jama’a ta hanyar kafar da ya yi amfani da ita wajen yin zargin ya gaggauta janye shi, ko kuma su garzaya kotu.

Iyalin sun bai wa Janar Musa mai ritaya wa’adin kwanaki bakwai daga ranar fitar da sanarwar, ko dai ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin nasa, ko kuma ya janye zargin gaba ɗaya tare da ba su haƙuri a bainar jama’a.

Sun ce idan ya gaza yin hakan, za su ɗauki dukkan matakan shari’a da doka ta tanada domin kare kansu daga zargin da suka kira marar tushe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata