Ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Mahadi Aliyu Gusau, ya musanta rahotannin da ke cewa ya janye daga takararsa ta gwamna a zaɓen da ke tafe.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaransa, Salisu Mohammed, ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo kan batun ƙarya ne kuma ba su da tushe.
A cewar sanarwar, wasu ‘yan siyasa ne masu son tayar da hankali da rikice-rikice a fagen siyasar jihar suka ƙirƙiri wannan jita-jita domin yaudarar jama’a da kuma raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Sanarwar ta jaddada cewa Mahadi Gusau shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Zamfara, kuma bai taɓa sanar da janye takararsa ba a kowane lokaci.
Ta kuma ce bai ba wani mutum ko ƙungiya izinin yin magana a madadinsa kan batun janye takara ba, don haka duk wata sanarwa ko rubutu da ke nuna akasin haka ya kamata a yi watsi da shi.
Salisu Mohammed ya yi kira ga mambobin jam’iyyar ADC, magoya baya, masu ruwa da tsaki da kuma hukumar zaɓen Nijeriya INEC da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni marasa tushe.
Ya ƙara da cewa Mahadi Gusau na ci gaba da gudanar da shirye-shiryensa na siyasa da tuntubar al’umma domin cimma burinsa na jagorantar jihar Zamfara.
Rahotannin janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ake samun sauye-sauye da ce-ce-ku-ce a wasu jam’iyyu.
