Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Nijeriya (NUT) ke yi, tana mai danganta matakin da matsalar rashin tsaro da kuma yawaitar sace malamai da ɗalibai a sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar ranar Laraba, ya ce yajin aikin na nuna irin takaicin da malamai ke ciki sakamakon ci gaba da hare-hare da garkuwa da mutane, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa Ajaero ya ce sace ɗalibai a jihar Oyo da sauran irin waɗannan hare-hare sun nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Nijeriya. Ya ƙara da cewa malamai da ɗalibai na ci gaba da zama cikin fargaba yayin gudanar da harkokinsu na ilimi.
NLC ta yi gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar matakan haɗin kai da NUT idan har gwamnati da hukumomin tsaro ba su ɗauki matakai na zahiri da za a iya auna tasirinsu ba wajen magance matsalar rashin tsaro.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda sace-sace da hare-haren masu ɗauke da makamai suka bazu zuwa jihohi kamar Zamfara, Plateau da Kogi, lamarin da ke jefa ayar tambaya kan tasirin matakan tsaron da ake ɗauka a halin yanzu.
Yayin da ta amince cewa hukumomin tsaro na fuskantar ƙalubale, NLC ta buƙaci gwamnatoci a matakai daban-daban su daina bayar da tabbaci kawai, su ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace da kuma kare malamai, ɗalibai da sauran ma’aikatan gwamnati masu rauni.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa idan hare-haren suka ci gaba, hakan na iya janyo cikas ga harkokin ilimi da sauran ayyukan gwamnati a faɗin ƙasar.
